Hukumomin lafiya na Saudiyya sun kaddamar da cikakken shiri na kula da lafiya a birnin Madinah domin tunkarar Hajjin shekarar 1447H, inda aka jibge sama da ma’aikatan lafiya 700 domin kula da maniyyata.
Tawagar ta kunshi likitoci, nas-nas (nurses), da jami’an agajin gaggawa da aka horas musamman kan kula da taron jama’a masu yawa. Za su rika aiki a jere (shift) domin tabbatar da ci gaba da bayar da kulawar lafiya a duk tsawon lokacin aikin Hajji.
An mayar da hankali wajen samar da ayyukan agajin gaggawa a harabar Masjid an-Nabawi da kuma manyan hanyoyin da maniyyata ke bi. Motocin asibiti guda 90 an tanade su a wurare masu cunkoso, yayin da jiragen agajin gaggawa ke cikin shiri domin daukar mataki cikin gaggawa idan bukata ta taso.
Haka kuma, an kafa cibiyoyin lafiya a muhimman wuraren da maniyyata ke taruwa domin saukaka samun kulawa cikin sauri.
Shirin zai fara ne daga watan Zul-Qa’ada 1447H har zuwa 15 ga Muharram 1448H, wanda ya kunshi dukkan matakan Hajji daga isowar maniyyata, gudanar da ibadu, har zuwa komawarsu kasashensu.
(II)

